Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sai Messi Ya Warke Daga Cutar COVID Zai Koma Faransa - Pochettino


Messi
Messi

Dan shekara 34, Messi ya ci wa PSG kwallaye 6 cikin dukkan wasannin da kungiyar ta buga a gasa daban-daban.

Dan wasan Paris Saint Germain Lionel Messi ya kebe kansa bayan da gwaji ya nuna cewa ya harbu da cutar Coronavirus.

Kungiyar ta PSG ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi a cewar Reuters.

Messi ya kebe kansa ne a kasarsa ta Argentina, kuma ba zai samu damar yin tafiya zuwa Faransa ba, sai gwaji ya nuna cewa ba ya dauke da cutar a cewar hukumomin kungiyar.

A cewar PSG, sauran ‘yan wasan da suka kamu da cutar akwai mai tsaron gida Juan Bernat, da mai tsaron raga na biyu Sergio Rico sai dan wasan tsakiya Nathan Bitumazala.

Wannan lamari ya faru ne yayin da PSG ke shirin karawa da Vanne a ranar Litinin a gasar French Cup.

PSG ce ke jagorantar teburin gasar ta Ligue 1 da maki 46 bayan da ta buga wasanni 19.

Hakan na nufin ‘yan wasan na Maurice Pochettino sun ba Nice da ke biye da su tazarar maki 13.

Dan shekara 34, Messi ya ci wa PSG kwallaye 6 cikin dukkan gasar da kungiyar ta buga.

A watan Agustan bara Messi ya koma PSG daga Barcelona.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG