Wannan mahajar mai suna 'Complete Care' da kungiyar likitoci suka kaddamar, sun bayyana cewa zai taimaka wajen inganta lafiya idan aka rage tsawon lokutan da majinyata ke batawa wajen ganin likita.
Bincike ya nuna cewa majinyata na kwashe sa'o'i fiye da biyu, a wata sa'in ma har yini guda domin ganin likita a asibitocin gwamnati da ke birane da kauyuka, sakamakon rashin isassun likitoci da za su kula da yawan marasa lafiyar da ake da shii a kowace rana.
Duk da cewa likitoci da dama sun yi na'am da wannan ci gaban, wasu na ganin har yanzu da sauran rina a kaba domin aiki na likita da kuma na marasa lafiya na bukatar haduwa ido-da-ido.
" Amfaninta ya tsaya ne ga cututtuka masu nasaba da kananan matsaloli kamar ciwon kai, ko zazzabi - shi ma zazzabin ya kunshi abubuwa da yawa, ko kuma ta yi wu marar lafiya an ba shi wani maganin ya sha amma sai yana bashi wata matsala, to zai iya amfani da manhajar domin sanar da likita." inji Dr Salihu Ibrahim
Dr Ibrahim ya kara da cewa baya ga wadannan matsalolin, yawancin cututtuka na bukatar ganin likita keke-da-keke domin gano inda matsalar ta ke kafin a iya maganceta.
Saurari cikakken rohoton wakilinmu Babangida Jibril
Facebook Forum