Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabuwar Jam'iyya a Koriya Ta Kudu Na Son Ban Ki-moon Ya Mata Takara


Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon
Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon

‘Yan majalisun Koriya ta Kudu 29 ne suka fice daga jam’iyya Saenuri mai mulkin kasar, saboda badakalar cin hancin da tayi sanadiyar tsige shugabar kasar Park Geun-hye daga mulki.

‘Yan majalisun dai sun kafa wata sabuwar jam’iyya, wadda suka kirata da suna New Conservative Party for Reform, ana kuma sa ran kaddamar da ita ranar 24 ga watan Janairun shekarar 2017 mai zuwa.

Sabuwar jam’iyyar dai na fatan samun goyon bayan masu ra’ayin mazan jiya, wadanda ba su ji dadin abin da ya faru a jam’iyya mai mulki ba, kafin babban zabe mai zuwa.

A wani bangaren yunkurin samun nasara, sabuwar jam’iyyar za ta yi kokarin shawo kan babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai barin gado Ban Ki-moon da ya tsaya a matsayin dan takararta.

Ban Ki-moon dai bai fadi ko zai tsaya takarar shugaban kasar ba, a wata hira da Muryar Amurka ta yi da shi kwannan nan, yace yau zai tsaida shawara kan abinda zai yi bayan ya bar matsayin babban magatakarda.

Ana daukar Ban Ki-moon a matsayin wanda ya fi dacewa ya yi takara a jam’iyyar masu ra’ayin mazan jiya, domin maye gurbin hambararriyar shugaba Park.

Binciken jin ra’ayin jama’a da aka gudanar na baya-bayan nan na nuni da cewa, Ban na gaba kadan da dan takarar jam’iyyar masu sassaucin ra’ayi Moon Jae-in, wanda ya sha kaye a zaben da akayi shekaru hudu da suka gabata.

XS
SM
MD
LG