Rahottanin dake shigowa daga kasar Syria sunce sabon yaki ya barke sa’oi biyu kacal bayan yarjejeniyar tsagaita wutar da aka kulla wadda ta soma aiki daga karfe goma sha-biyun dare, agogon Syria din.
Sai dai yarjejeniyar an kulla ta ne kawai tsakanin gwamnatin Syria da wasu kungiyoyin ‘yan tawaye, amma banda kungiyoyin dake da alaka da ISIS.
Wata kungiyar ‘yan Syria dake zaune a kasashen waje mai suna “Observatory”, tace ‘yantawayen ne suka soma karya ka’idojin yarjejeniyar sulhun lokacinda suka yi kokarin kama wasu wurare dake lardin Hama.
To amma kuma Mohammed Rasheed, mai magana da yawun wata kungiyar ‘yantawaye mai suna Jaish-al-Nasr, yace sojan gwamanti ne suka fara karya yarjejeniyar tsagaita fadan lokacinda suka fara cilla rokoki akan wasu yankuna dake lardin Idlib dake makwaptaka da lardin Hama din.
///ALIYU: NEWS BREAK///