Babban bankin ya bayyana cewa, ba wai an yi sabon tsarin ne don kuntatawa 'yan kasa ba illa komawa tsarin rage yawan takardun kudi da ake hada-hada dasu a koma tsare-tsaren hada-hada na zamani wato cashless policy don karawa takardun kudin kasar daraja ya iya yin gogayya da sauran takardun kudi.
Babban Bankin ya bayyana hakan ne a yayin hira ta musamman da muryar Amurka a birnin tarayya Abuja, ta bakin daraktan hada-hadar kudin bankin, Mal. Ahmed Bello Umar, inda bankin yace za’a fara aiwatar da komawa tsarin na’urar cire kudi ta ATM da zai rika fitar da takardun kudi daga naira 200 zuwa kasa ne daga ranar 9 ga watan Janairun shekarar 2023 mai zuwa.
A cewar Mal. Ahmed Bello, aikin mayar da na’urar cire kudi na ATM zuwa naira 200 zuwa kasa ba zai dauki wani lokaci ko lakume wasu kudadde ba illa a shiga ta na’urar bankuna a yi gyaran tsarin ya fara fitar da irin kananan takardun kudi da ake san na’urorin su rika fitarwa don janye takardun kudi na naira dubu 1 da dari biyar daga cikin tsarin hada-hadar kudi a kasar.
Babban bankin ya kara da cewa, ba wai an hana al’ummar kasa cire kudaden su daga banki ba, illa su koma tsare-tsaren zamani na na’ura kuma idan har mutum na son cire tsabar kudi da suka wuce wanda aka kayyade na naira dubu 100 a duk sati ga mutum guda ko dubu 500 ga kamfanoni a cikin banki, mutum zai biya kaso 5 cikin 100 na kudadden da zai cira, kuma idan ana son gujewa hakan sai a bi ta tsarin banki a intanet a yi hada-hadar da ake da bukatar yin.
Haka kuma, darakta Ahmed Bello na bankin CBN ya ce bankin na sa ran hada-hadar da za’a yi a lokutan bukukkuwan kirsimeti zai taimaka wajen yawan kudadden da ke yawo a cikin kasar su ragu sosai kafin a kai lokacin da za’a janye sabin kudadden daga cikin kasar.
A game da ‘yan kasa su shiga tsarin banki na yau da kullum da kuma na yanar gizo wato E-Naira da aka kaddamar a watan Oktobar bara, bankin CBN ya ce ya zamo wajibi dukannin ‘yan Najeriya su bude asusun bankuna don zamani ne ya zo da hakan.
A saurari bayani cikin sauti: