Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Shugaban Amurka da Mataimakinsa Sun Gana A New York


Sabon shugaban Amurka Donald Trump da Mataimakinsa Mike Pence
Sabon shugaban Amurka Donald Trump da Mataimakinsa Mike Pence

A jiya ne sabon shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump da mataimakinsa Mike Pence suka yi wani zaman tattaunawa a birnin New York don ci gaba da tsara yadda zasu cike gurabun manyan mukaman gwamnatin tasu.

Shugabannin biyu suna bukatar su cike gurabu sama da 4,000 na mukaman ma’aikatun gwamantin tasu daban-daban kafin ranar 20 ga watan Janairun shekara mai zuwa lokacinda zasu dauki rantsuwar kama aiki.

Abinda Trump da mataimakin nasa suka fi baiwa fifiko a yanzu dai shine nada shugabannin Ma’akatun Harakokin Waje, Tsaro, Atgone-Janar da kuma Hukumar Tsaro ta cikin gida ta kasar.

Dukkan wadanan mukaman ana kallonsu a matsayin alamomin da zasu nuna wa duniya irin kamun ludayin sabuwar gwamnati da kuma alkiblar da zata dauka wajen yaki da akidar ta’addanci.

Wasu daga cikin mukarabban Trump sun ce mai yiyuwa ne a nada tsohon Magajin Garin New York, Rudy Giuliani a matsayin sabon Sakataren Harakokin Wajen Amurka koda yake bai taba wani aiki mai alaka da diplomasiya ba.

XS
SM
MD
LG