Bayan da ya yi balaguron aikin diflomasiyyarsa na farko da zuwa Brussels, inda ake taron Ministocin kasashen da ke cikin kungiyar kawance ta NATO, sabon Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya yada zango a Gabas Ta Tsakiya a yau dinnan Asabar.
Ziyarar ta kwanaki uku ta hada da yada zango a Saudiyya da Isira’ila da Jordan, inda ake kyautata zaton zai yi bayani ga kawayen Amurka kan manufar Amurka game da Iran.
Jiya Jumma’a Pompeo y ace har yanzu ba a yanke shawara kan ko Shugaba Donald Trump zai janye daga yarjajjeniyar da aka cimma da Iran kan nukiliya ko a’a, ya kara da cewa har yanzu ana cigaba da tattaunawa.
A wani taron manema labarai na farko tun da ya fara sabon aikin nasa, Pompeo y ace, “Muddun ba a yi wata gagarumar gyara ba, muddun ba a daidai al’amura ba, wato raunin wannan yarjajjeniyar, Shugaba Trump ba zai cigaba da kasancewa cikin ta har bayan watan Mayu
Facebook Forum