A kalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu a rigingimun baya-bayannan a kudancin Jihar Taraba, wanda yaki ci, yaki cinyewa.
Kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana, maharani sun kai hari ne a wasu kauyuka uku na yankin Ukari dake kudancin Jihar Taraba inda aka samu asarar rayuka fiye da 20, baya ga dukiyar da aka barnata.
Wani wanda yaso a sakaye sunanshi, cewa yayi “da suka zo da Asuba, an kashe mutane yara da mata su 21. Fulani ne, suna yaren Fulani muna jinsu.”
Shima wani dan Majalisar dokokin Jihar dake wakiltar mazabar Wukari, Ishaya Daniel Gani, inda ya tabbatar da wannan harin da aka kai.
“Su Fulani, sun zargi cewa an sace musu shanu, an kwashe musu shanu, sun zo sun samu garin Tumari baki daya, sun kona gonakin shinkafar gaba daya”.
Kawo yanzu an tura Jami’an tsaro zuwa yankin inda kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Taraba ASP Joseph Kuji yake cewa mutum guda ne kawai aka kashe.
“Da muka samu labari a take, muka tura ‘yan sanda da kuma Mobilawa zuwa wannan wajen.
Sai dai kuma hadakar Kungiyar Makiyaya ta Miyatti Allah ta musanta zargin da akeyi na cewa makiyaya ne suke kai wadannan hare-hare. Alhaji Mafindi Umar DanBuram dake zama shugaban kungiyar Miyatti Allah a Jihar Taraba, yayi bayanin irin barnar da aka yiwa Fulani.
“A gaskiya, mu bamu da sanin wani hari da aka kai daga wajen kungiyar mu ta makiyaya. Sai dai makon da ya wuce, mun san lallai jukunawa sun kira taro, amma a wannan lokaci ne kuma aka kashe Fulani aka debi shanunshi.”
To ko me shugabanni suke yi a wannan yanki domin wanzar da zaman lafiya? Ishaya Daniel Gani dan majalisar dokoki ne.
“A yanzu mun dauki matakan tsaro. Dole ne mu nemi hanyar da zamu sasanta wannan abu.”