Kimanin mutane dubu arba'in da biyar ne, mazauna kauyukan dake kewaye da Kandaji garin da za'a gina madatsar ruwan zasu rasa muhallansu kazalika wasu dubu kuma dake bangaren Mali aikin zai shafa.
Wato mutane 55,000 a kasashen biyu ne za'a tilastawa barin garuruwansu wadanda dole ne a sake tsugunar dasu tare da sake gina masu muhallansu da wuraren jin dadinsu.
A karkashin kwamitin dake bin digdigin ayyukan gina madatsar ruwan, gwamnatin Nijar ta tattauna akan hanyoyin da za'a bi a sake ginawa mutanen da aikin ya shafa gidajensu da kuma cigaba da aikin. Akwai kuma batun biyan diyya ga mutanen da abun ya shafa.
Ministan fadar shugaban kasar Nijar yace sun kuma tattauna akan yadda za'a ba mutanen gonakai da zasu noma. Bisa ga alamu kamar yadda ministan ya bayyana gwamnati ta shirya tsaf ta ba kowa hakkinsa.
Tsarin gina madatsar ruwan ya samu amincewar bankuna sama da goma wadanda aka tattauna dasu akan gina sabbin garuruwa tare da gina makarantu da wuraren ibada da asibitoci da hanyoyi da dai sauransu.
Aikin zai lakume miliyan dubu da dari daya na dalar Amurka. Watan Agustan dake tafe ne za'a fara aikin.
Mai magana da yawun masu hannu da shuni Mudi Tarhuni yace sun gamsu da duk abubuwan da aka tsayar a taron. Sai dai yace ba zasu fara aikin ba sai sun tabbatar komi ya kankama, musamman sake zaunar da mutanen da zasu rasa muhallansu.
Daga shekara mai zuwa har zuwa ta 2020 zasu dage haikan kan gina madatsar kuma a soma anfani da ita a shekarar 2021.
Madatsar zata taimakawa Nijar da kasashen dake makwaftaka da ita wurin inganta noma, kiwo da samar da wutar lantarki. da wadatar da cimaka.
Ga karin bayani.