Wadannan kudaden an fitar dasu ne tsakanin watan Janairun zuwa Disamban 2015 lokacin da Ahmadu Salifu ke rike da mukamin kakakin majalisar da nufin gyare gyaren gidan da gwamnati tayi tanadi domin kakakin majalisar.
Kodayake kwamitin 'yan majalisar bai amince a yi sokaci akan rahoton binciken nasa ba, kungiyar dake yaki da cin hanci da rashawa ta Transparency International ta bakin sakatarenta Mamman Wada, ta fara kiran a kara yin bincike mai zurfi kan badakalar.
Mamman Wada yace an yi bincike an ga tsohon kakakin majalisar ya gyara gidan gwamnati da sefa miliyan dari bakwai kana ya gyara gidan kansa da sefa miliyan talatin ko kuma nera miliyan goma sha hudu. Bugu da kari kakakin wai a lokacin yana karban kudin haya. A kungiyance sun ce a garzaya kotu ta yi bincike idan kuma an samu mutum da laifi a hukumtashi ko shi wanene.
Shugaban wata kungiya Nuhu Muhammadu Arzika yace da zara an tabbatar da binciken to yakamata hukumomin Nijar su yi koyi da abun da ya faru a Afirka ta Kudu. Yace idan har ya karbi kudi ya gyara gidanshi kuma an bashi gidan gwamnati ya zauna to an yi ba daidai ba. Abun da ya faru ke nan a Afirka ta Kudu. Shi ma ya kamata a tilasta mashi ya mayarda kudin da ya diba.
Wata kungiyar tace zata sa ido ta ga yadda za'a yi da maganar idan kuma ta ga ana jankafa to zata rubutawa shugaban kasa Mahammadou Issoufou kamar yadda aka tsara kungiyar ta ba shugaban kasa bayanin duk wata almundahanar da suke da masaniya a kanta.
Ga karin bayani.