Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Bincike Ya Nuna Yadda Aka Kashe Sojan Amurka a Nijar


Sojojin Amurka da aka kashe a Jmahuriyar Nijar, La David (Dama)
Sojojin Amurka da aka kashe a Jmahuriyar Nijar, La David (Dama)

Sabbin bayanai sun yi karin haske kan kisan da aka yi wa sojojin Amurka 4 a Jamhuriyyar Nijar, musamman La David Johnson da aka tsinci gawarsa daga karshe.

Wani binciken da sojojin Amurka suka gudanar ya bayyana cewa an harbi sojan Amurka da ‘yan ta’adda suka kashe a Jamhuriyar Nijar sau 18 kuma shi ma ya mai da martini kafin ya mutu.

Jami’an Amurka ne suka bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press hakan, a wani binciken da ba’a kammala ba na kisan da aka yi wa Saje La David Johnson.

Har ila yau wasu sojoji uku na Amurka sun rasa rayukansu a harin wanda aka kai a kusa da iyakar Nijar da Mali.

Harin da kuma mutuwar Johnson sun haifar da rudani da dama inda ake dasa alamar tambaya kan dalilin da ya sa aka samo gawarsa kusan kilomita biyu daga inda abin ya faru da kuma yadda aka yi ba a samu gawarsa ba sai bayan kwanaki biyu.

A cewar kamfanin dillancin labarai na AP, sojojin Jamhuriyar Nijar biyu da kuma Johnson sun yi kokarin guduwa daga wurin harin da nufin samun kariya a jikin wata mota kirar Jeep, amma kuma aka harbe sojojin na Nijar kafin su karasa wajen motar.

Bayanai sun yi nuni da cewa shi Johnson wanda ke da cikakken horo ya samu damar buya a jikin wani abu, sannan sai da suka yi ba ta kashi da maharan kafin su kashe shi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG