Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rwanda Za Ta Fitar da Sabbin Ka’idojin Dakile Yaduwar COVID-19


A yau Talata ake sa ran hukumomi a kasar Rwanda za su fitar da sabbin ka’idojin dakile yaduwar annobar coronavirus, bayan wani tsari da ta fitar a ‘yan kwanakin baya da su ka hada da samar da wata mota da ke gwaji ga mutane da ke yawo a cikin kasar.

Matakin na kasar ya yi daidai da irin matakan da kasashen gabashin Afrika ke dauka, inda aka fara samun mace-mace a sanadiyyar annobar coronavirus a cikin ranakun hutun karshen mako.

A ranar Lahadin da ta gabata an sami sabbin wadanda su ka kamu da cutar a Rwanda da su ka kai mutum 11, inda kuma aka sami mutum na farko da ya mutu sanadiyyar cutar a kasar.

Kasar kuma ta cimma matsayar dakatar da tafiye-tafiye a motoci daga wani yankin zuwa wani, har zuwa birnin Kigali duk a cikin yunkurin dakile yaduwar annobar.

Kasar Rwanda na da mutane 370 da su ka kamu da wannan cutar, ya zuwa yanzu kuma,mutum 1 ne kawai ya mutu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG