A Jamhuriyar Nijer wasu ‘yan kasar sun fara bayyana ra’ayoyinsu, bayan da majalisar dokokin kasar ta amince da hukumomi su fara sauraren hirar wayoyin salula na jama’a cikin sirri ko bibiyar masu amfani da kafafen zamani da nufin tatsar bayanai a matsayin wata hanyar ta yaki da ta’addanci.
‘Yan hamayya na cewa matakin na da nasaba da yunkurin rufe bakin masu sukar manufofin gwamnatin shugaba Issouhou Mahamadou.
An bayyana dokar a matsayin wani matakin yaki da ta’addanci domin daukar hanyoyin zuba ido akan wadanda ke kokarin tada zaune tsaye a kasar, sakamakon lura da yadda wasu suka mayarda kafafen sada zumunta tamkar wani makamin cin zarafi ko yiwa abokan hamayyar siyasa kazafi inji gwmnatin Nijer.
Editan jaridar Le Temps Zabeirou Souley ya ce, yana goyon bayan wannan yunkuri na gwamnati. Shugabar kungiyar matasa ta JENOM Hajiya Falmata Taya tace, tasirin wannan doka ya dogara ne da hanyoyin da za a yi amfani da ita.
"Rashin lakantar ainahin amfanin hanyoyin sadarwar zamani a wajen al’umma da rashin amfani da hanyoyin ga hukumomi domin wayar da kan jama’a akan manufofin da suka sa gaba, su ne masababin wannan ce-ce-ku-ce akan wannan sabuwar doka" inji shugaban kungiyar AJEPA Laouali Tsalha.
A nan gaba kadan ake sa ran shugaban Nijer Issouhou Mahamadou zai rattaba hannu akan takardun zartar da wannan doka da ta sa ‘yan adawa ficewa daga zauren majalisa a dai-dai lokacin da bangarori ke mahawara a kan ta a karshen makon da ya gabata saboda a cewarsu, ba sa goyon bayan matakin tauye hakkin ‘yan kasa.
Saurai Karin bayani cikin sauti daga Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum