Rundunar 'yansandan jihar Oyo ta gano tare da kamo wadanda suka afkawa gonakin makiyaya suka tafka masu hasarar miliyoyin nera.
Lamarin ya faru ne a garin Igaga cikin karamar hukumar Aiyete.
Alhaji Muhammad Musa Katsina kwamishanan 'yansandan jihar yace ya je gonakin kuma ya ga irin barnar da aka tafka. Yace ya ga kadada dari da goma sha daya na gonakin da aka bata. Masara dake gonakin har ta fara goyo haka ma wake da doya da dai sauransu.
Mutanen da suka yi barnar sun shiga da tratoci ne cikin dare. Mai unguwar kauyen shi ya taimaka aka gano wadanda suka haddasa ta'asar. 'Yansada sun kamosu kuma sun amince da aika-aikar da suka yi.
Mutanen da suka aikata laifin
basu da wata hujjar yin hakan sai dai sun ce filin nasu ne. Amma su makiyayan ba yau suka fara noman filin ba. Sun yi wajen shekaru goma sha biyar suna noma kan filin.
Wurin gwamnati ce ta kebe saboda aikin noma, wurin da manoma ka iya zama su yi aikin noma.
Dattawan garin sun ba 'yansanda hadin kai kwarai shi ya sa aka iya gano masu laifin domin wadanda suka haddasa abun manyan mutane ne.
'Yansanda sun yi bincike akan mutanen tare da samun shaidu cewa sun aikata barna cikin ganganci.
An gurfanar da mutanen gaban shari'a kuma yanzu suna gidan kaso
Masu gonakin da aka zanta dasu sun yi kiyasin kudin anfanin gona da aka lalata sun fi nera miliyan talatin da biyar.
Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal.