A halin yanzu mutanen jihar Oyo musamman a babban birnin jihar, Ibadan suna fama da matsanancin karancin man fetur.
Karancin man ya yi sanadiyar wasu mutane suna kwana a gidajen man suna jiran gawon shanu. Wani da yayi kwanaki biyu a gidan mai yace ya zama masa dole domin idan bai sami man ba babu abun da zai iya yi. Wani kuma da ya zanta da Muryar Amurka yace tafiya cikin gari ko yin balaguro yayi wuya.
Wani kuma da ya fusata tace "muna da abu kuma muna shan muguwar wahala a kansa" Yace shi bai gane ba.Wani kuma mai hawan babur yace yanzu ana sayar da lita daya ta mai nera dari biyu ko dari biyu da hamsin.
Talakawa na shan wahala kuma za'a cigaba da hakan idan gwamnati bata dauki matakan gaggawa ba ta shawo kan lamarin.Karancin man fetur dai yayi sanadiyar tashin farashen kaya da kudin sufuri.
Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal.