Kwamishanan ya bayyana hakan ne a birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno yayinda yake kaddamar da wani shiri mai taken "Canji Zai Fara daga Kaina".
Kwamishanan shi ne jami'in 'yansanda na farko da ya kaddamar da shirin. Shirin ya samu halartar duk jami'an 'yansanda dake aiki a karkashin kwamishanan da 'yan jarida da jami'an gwamnati da sauran al'umma.
Mr. Daniel Chukwu ya kara da cewa zasu kama duk wani dansanda da suka kama yana karya doka wajen gudanar da aikinsa kamar cin hanci ko neman na goro daga jama'a.
Inji kwamishanan beli kyauta ne koina ba sai mutum ya biya ba. Bayan kaddamar da shirin yace zasu fitar da bayanan fadakar da jama'a cewa beli kyauta ne koina mutum yake. Duk dansandan da ya nemi a bashi kudi kafin ya bada beli kwamishanan yace a kirashi.
Matakan da rundunar zata dauka akan duk wani jami'inta da ya karya duka sun hada da rage mukami ko kora daga aiki gaba daya.
Kwamishanan shari'a na jihar Borno wanda ya wakilci gwamnan a wurin kaddamar da shirin yace abun farin ciki ne cewa su 'yansandan suka fito da shirin ganin yadda kasar gaba daya take kallon 'yansandan kasar.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.