Rundunar 'Yan sandan babban birnin Tarayyar wacce dama tuni ta kaddamar da wani farmaki a kan duwatsun dake zagaye da babban birnin Tarayyar, biyo bayan samun bayanan sirri ta kai samame a wani daji dake kan iyakar Abuja da jihar Niger.
Da ya ke wa Sashin Hausa na Muryar Amurka bayani, Kwamishinan 'Yan sandan yankin babban birnin Tarayyar Najeriya CP Babaji Sunday yace akwai wasu kauyukan yankin Karamar Hukumar Abaji da ake kira Yaba/Adaba inda yan bindigar dake satar mutane suka kafa sansani a wannan daji.
Bayan kai wani mummunan farmaki ne kuma 'Yan sandan suka cafke wani dan bindigar wanda bayan gudanar da bincike kuma ya kai ga kara kamo sauran yan bindigar a wannan daji da yan ta'addan sukai kakagida.
CP Babaji yace sun kwato wata babbar bindiga mai sarrafa kanta wato GPMG wacce ka iya tada gari da kuma karin wasu bindigogin kirar AK 49, da AK 47, da kuma wata karamar bindiga kirar Pistol da ma dimbin harsasai masu rai
Bisa binciken farko da rundunar yansandan ta aiwatar, yan bindigar sun ce su suke addabar yankuna Kuje, Kwali da Abaji dake kudancin birnin Abuja da kuma ke kan iyaka da jihohin Niger, Kogi da Nasarawa.
Kwamishinan 'yan sandan yace sun sami labaran sirri dake nuna yan bindiga sun zagaye birnin, abin kuma da yasa suka kaddamar da wani gagarumin farmakin kwana uku da hadin gwiwar sauran jami'an tsaro inda suka fatattakesu'
Tuni masana tsaro irinsu Dr Kabiru Adamu ke jinjina hobbasan Yansandan, yana mai cewa matukar aka ci gaba da tattara bayanan sirri, tantancewa da aiki dasu, to ba shakka za a sami nasarar kawo karshen aika aikar yan bindigar dake satar mutane don neman kudin fansa.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: