Kakakin sojojin ruwan Najeriya Navy Commodore Sulyman Dahun ya shaidawa Muryar Amurka cewa, wasu ‘yan fashin Teku su goma ne suka yi garkuwa da jirgin kamun kifi a ruwan kasar Cote d'voire kuma suka shigo Najeriya dashi.
Hukumar dake sa ido kan sufurin ruwa ta duniya ta ankarar da rundunar mayakan ruwan Najeriya inda su kuma suka yi wa jirgin kofar rago a daidai lokacin da ya iso kasar.
Ya zuwa yanzu dai an ceto wannan jirgi samfurin HEILUFENG II tare da tserar da ma'aikatan jirgin su goma sha takwas wadanda ‘yan asalin kasashen China, Cote d'voire da Ghana ne, sannan kuma an cafke ‘yan fashin.
Rundunar mayakan Ruwan Najeriya tace, a halin yanzu tana ci gaba da gudanar da bincike tare da tatsar bayanai daga ‘yan fashin tekun, tuni kuma an kawo jirgin a sansanin mayakan ruwan Najeriya dake Lagos.
Wannan shine karo na biyar a jere da dakarun ruwan Najeriya su ke ceto jiragen ruwan kasashen waje da ake garkuwa dasu a wajen ruwan kasar, al'amarin da masanin tsaro kwamanda Baba Gamawa ya ce, yana nuna amfanin alakar aiki tare tsakanin sojojin ruwan kasashen Afirka ta yamma.
Saurari Karin bayani daga Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum