Rundunar sojojin Kenya ta bada labari cewa ta kama wani gari a kudancin Somalia daga hanun mayakan sakai na kungiyar al-shabab, a wani matakin soja da ta dauka tare da hadin guiwar sojojin Somalia.
A wani sako da ta buga a dandalin Twitter, kakakin rundunar mayakan Kenya Emmanuel Chirchir, yace sun kama garin Fafadun a wani harin da suka halaka mayakan al-shabab uku.
Chirchir yace cikin mayakan al-shabab da aka kashe har da wani shugabanta a yankin Gedo Sheikh Hassan Hussein. Yace an jikkata wani sojan Kenya daya, sai dai raunin nasa ba mai tsanani bane.
Cikin watan oktoban bara ne sojojin Kenya suka kutsa cikin Somalia domin fatattakar al-shabab, kungiyar da take rike da yankuna masu yawa a kudanci da kuma tsakiyar Somalia. Kenya tana zargin kungiyar da tsallakawa ta cikin kasarta su sace mutane.
Kungiyar tana fuskantar matsin lamba daga sojojin kiyaye zaman lafiya na tarayyar Afirka wadanda suka koresu daga babban birnin kasar Mugadishu cikin watan Agusta, haka Ethiopia ma tana matsawa kungiyar lamba har ta kwace garin Beledweyne ranar Asabar.