Shedun gani da ido a kasar Somaliya sunce sojojin Ethiopia sun tilastawa yan yakin sa kan kungiyar Al Shabab arcewa daga birnin Beledweyne dake kan iyakar kasar.
Mazauna birnin Beledweyne sunce a yau asabar yan yakin sa kan kungiyar Al Shabab suka arce kafin isowar sojojin Ethiopia.
Wasu mazauna birnin sunce sunji karajin harbe harbe a wajen birnin, to amma ba’a tabbatar da rahoton ko wani ya jikatta daga dukkan bangarorin ba.
Birnin Beledweyne yana tazarar kilomita talatin daga kan iyakar Somaliya. A yan watanin da suka shige birnin ya sha fadawa hannun bangarori dabam dabam, a yayinda wasu yan yakin sa kai ke kokarin mamaye shi.
Harin na yau asabar ya zama shine wuri na uku da aka kalubalanci yan yaki sa kai.
Tun dai lokacinda aka hambarar da gwamnatin Mohammed Siad Barre a alif dari tara da casa’in da daya, kasar Somaliya ta kasance babu tsayayiyar gwamnati.