Tarzoma tsakanin matasan Falasdinu da 'Yansandna Isra'ila ta kara tsanani a jiya Asabar a Hebron a yamacin kogin Jordan, da birnin kudus, rahotannin da 'Yansandan suka bayar na cewa akalla matasa hudu dake dauke da wukake ciki harda wata budurwa 'yar shekara 16 da haifuwa, suna cikin wadanda aka kashe a lamura daban daban. Hukumomi suka ce jami'an tsaron kasar da dama sun ji rauni a hare haren.
Akalla Falasdinawa 40 da yahudawa 7 suna daga cikin wadanda suka halaka a makonnin da aka yi ana tashe tashen hankula da jami'an yankin Falasdinu suke danganatawa da kkarin da Yahudawa suke yi na amfani da masallacin al-Aqsa wuri na uku a daraja ga musulmi wand a yahudawa suke kira Temple Mount. Isra'ila ta dage cewa kariya ne ikirarin da Falasdinawa suke cewa tana kokarin karbe masallacin.
Shugaban Amurka Barack Obama da yake magana jiya ranar jumma'a ya bayyana damuwa kan tarzomar, daga nan yayi kira ga shugabanni d a suke yankin suyi kokarin hana ko a daina amfani da kalamai da zasu tada tarzoma ko fusatar da jama'a ko ya janyo rashim fahimtar juna.
Shugaban na Amurka yace ya ragewa shugabannin Falasdinu da Isra'ila idan har suna son su koma teburin shawarwari. Ya kara d a cewa a shirye Amurka take ta taimaka wajan sake farfado da danganataka mai ma'ana tsakanin sassan biyu.
Ana sa ran sakataren harkokin wajen Amurka John kerry zai gana da PM Isra'ila cikin makon nan.