Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Siyasar Kasar Kenya Na Kara zafi - Jami'ar Hukumar Zabe Ta Ajiye Aiki


Kungiyoyin kare hakkokin bil'adama sun ce an kashe mutane dayawa a lokutan zanga zanga tun bayan zaben shugaban kasa da aka yi a kasar ta Kenya.

Wata jami'ar hukumar zaben kasar Kenya tayi murabus mako daya kafin a sake zaben shugaban kasa da ake shirin yi, abinda ya kara ruruta wutar rikicin siyasar kasar dake gabashin Afrika.

Roselyn Akombe ta fidda wata sanarwa daga birnin New York dake nan Amurka yau Laraba, ta na mai cewa "zaben da ake shirin sake yi ranar 26 ga watan Oktoba ba zai cimma mizanin da ake fatan gani ba a zaman sahihin zabe." Akombe ta ce hukumar zaben dake tsaka-mai wuya, wadda ake kira IEBC a takaice, na fuskantar matsaloli na cikin gida da kuma barazana daga ‘yan siyasa.

Akombe ta kara da cewa "hukumar zaben tana da hannu a rikicin dake faruwa a halin yanzu." Ta kuma yi kira ga sauran tsofaffin abokan aikinta akan su nuna bajinta wajen bayyana abinda ke faruwa.

Akombe ta fadawa BBC cewa ta gudu daga Kenya bayan barazana dayawa da ta samu akan tsaro da lafiyarta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG