Biyo bayan rikicin kabilar da aka yi kwanan nan a garin Tingno da karamar hukumar Lamurde da ke jihar Adamawa, adadin ‘yan gudun hijira a sansanin Kupte da ke Lafiya na karuwa, kuma akasarinsu mata ne da yara.
Wasu ‘yan gudun hijirar da aka kashe mazajensu sun bayyana cewa suna cikin mawuyacin yanayi sun kuma yi kira ga gwamnati da ta kawo masu dauki.
Magritte Obidah, jami'ar kiwon lafiya ce da ke duba wadannan ‘yan gudun hijirar ta ce ya zuwa yanzu sun duba marasa lafiya fiye da dari da hamsin a sansanin da aka tanadar baya ga wadanda aka wuce da su manyan asibitoci da ke Lamurde da kuma Numan.
Da yake bayyana irin kokarin da suke yi a yanzu, Honarable Abubakar Yahaya, kansila mai wakiltar mazabar Lafiya wanda kuma shine shugaban wannan sansanin ya bukaci gwamnati da ta kara kawo masu taimakon gaggawa don a rage wa ‘yan gudun hijirar radadin yanayin da suke ciki, ya ce su na bukatar abinci, sutura da kudin kashewa.
Shi ma basaraken yankin da Yan gudun hijirar ke zaune a yanzu, Chief Jonathan Alfred ya ce zasu ci gaba da taimaka wa ‘yan gudun hijirar ko da yake har yanzu akwai kalubale musamman na karancin ruwa kuma sansanin ya yi kadan.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti daga Ibrahim Abdul'aziz:
Facebook Forum