Rikicin ya biyo bayan kasa cimma matsaya tsakanin ‘ya’yan jam’iyar APC kan batun shugabancin kwamitoci da wadansu suke gani wadanda aka ba basu dace ba. Yan jam’iyar APC a majalisar dai sun shiga wani zaman sirri tsakaninsu da nufin samun masalaha, amma hakan bata yiwuwa ba aka tada rikici har da kusan sake ba hammata iska.
Wadansu ‘yan majalisar suna nema ne a sauke shugaban masu rinjaye na majalisar, yayinda wadansu kuma ke korafin cewa, kakakin majalisar Yakubu Dogara, bai yi daidai ba a wajen raba mukamai.
A bangaren majalisar dattijai ma lamarin haka yake, domin kuwa wadansu ‘yan majalisar sun gana da manema labarai inda suke korafin cewa, shugaban majalisar Bukula Saraki bai bi tsarin majalisa wajen raba mukamai ba.
Wadansu ‘yan majalisar dai na korafin cewa, kasancewa maganar bin dokokin majalisa na kotu, duk wanii kwamiti da za a kafa, ko kuma nada shugabanni, ya sabawa doka, domin bisa ga cewarsu, shi kanshi shugaban majalisar dattijan ba bisa doka yake rike wannan kujerar ba.
Ga bayanin wakiliyar Sashen Hausa a Abuja, Madina Dauda