Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rayuwa A Kauyen da Ya Fi Kowane Wuri Sanyi A Duniya


A kauyen da ya fi ko ina sanyi a duniya, girar mutum tana daskarewa ta zamo kankara, abinci na zamowa kankara, yayin da numfashi ke daskarewa da zarar ya fita daga hancin mutum.

A kauyen Oymyakon mai mutane 500 a yankin Yakutia na kasar Rasha, mutane ba su iya kashe motarsu ko da ba su amfani da ita a saboda baturinta na iya mutuwa kwata-kwata saboda tsananin sanyi idan suka kashe motar.

Girar mutum ta kan daskare ta yi kankara daga numfashin da ya fito hancin mutum, ko kankara ta taru a gashin baki, duk da cewa kusan ya zamo dole mutum ya rufe ko ina a jikinsa, har fuska, musamman idan ana iska a lokacin sanyi.

A ranar lahadi da ta shige. na'urar auna sanyi (thermometer) da kauyen ya saya ya kafa a cikin gari don duk mai wucewa ya iya ganin irin matsayin sanyin da ake yi, ta lalace ta fashe, a lokacin da awun sanyi ya kai mizani 88 a kasa da mizanin daskarewar ruwa.

A lokacin hunturu a wannan kauye, kwata-kwata awa 3 kacal rana take yi a sama, watau daga fitowarta har zuwa faduwarta. Ana zama cikin duhun dare na tsawon awa 21.

Irin wannan tsananin sanyi yana shafar kowace irin rayuwa ta mutanen wannan yanki. Alal ga misali, a lokacin hunturu kamar a yanzu, akasarin abincinsu nama ne, wanda a wani lokacin a daskarensa suke ci haka, saboda ba a iya shuka komai a kasar wurin wadda take daskarewa ta zamo kamar kankara.

Wasu daga cikin irin wadannan abinci sun hada da wanda suke kira Stroganina, watau kifin da aka fere namansa kamar kilishi, amma danye wanda ya daskare ya zama kankara. Haka kuma su na cin naman wata dabba dangin barewa da aka fi samu a dazuzzukan wurin; da kuma hantar doki da ta daskare ta zamo kamar kankara.

Ba a iya tono a sanya bututun ruwa ko na bahaya a wurin, saboda haka duk wuraren bahaya, dakuna ne kawai ake yi a rufe su a baya ko gefen gidaje.

A lokacin hunturu, mutane ba su iya aiki na lokaci mai tsawo a waje, sai dai su yi kamar mintoci 20, sai su koma ciki, bayan kamar awa daya su sake fitowa su yi minti 20.

Wannan kauye na Oymyakon a shekarun 1920 da 1930 ya kasance zango na makiyayan bareyi dake tsayawa don shayar da dabbobinsu a saboda akwai wata mabubbugar ruwan zafi da bakinta ba ya daskarewa a wurin.

Idan aka yi rasuwa a wannan kauyen, sai an samu wuta an hura an gasa inda za a tona kabari kafin a iya samun sukunin binne mutum.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG