Abin da ya fi jan hankalin ‘yan Najeriya yanzu shine kwangilar gyaran filin jirgin saman Abuja, da aka kammala kafin cikar wa’adin da aka yanke masa. A cewar mallam Garba Shehu, filin jirgin saman Abuja na da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin kasar.
Hakan yasa gwamnatin tarayya ta tabbatar da ganin ta ware kudaden da ya kamata ayi aikin kafin a fara.
Sai dai kuma Alhaji Mutari Yerima sarkin Babarawa, ya yi korafi ne kan yadda ake bayar da aikin kwangiloli, kullum sai dai a kawo wata matsala ta daban. Amma yanzu sai gashi da yake aikin filin jirgin sama ne da manyan kasar ke hawa an kammala shi cikin gaggawa.
Shi kuma Abdulmajid Dan Bilki kwamanda na ganin ba haka batun yake ba, inda ya ce a karkashin gwamnatin shugaba Buhari, dukkan abin da aka ga ba a kammala shi ba to sai dai in an hadu da matsala. Haka kuma maganar gyaran filin saukar jirage dole ne ta zama gaba ganin yadda jiragen kasa da kasa ke sauka, kuma ya zama wajibi a gyara ta don a samu kwanciyar hankali a kasa.
A daya bangaren kuma, Sabo Imamu Gashiwa, na ganin akwai wasu abubuwa da suka fi gyaran filin saukar jiragen sama muhimmanci musamman gyaran hanyoyin da suka dade aka sa su a kasafin gyara aka kasa yi.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum