Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha zata rage kashe kudi akan tashar kasa da kasa ta sararin samaniya


Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin

Kafofin yada labaran kasar Rasha sun ce, gwamantin kasar na shirin rage kudaden da ta ke kashewa a tashar kasa da kasa da ke kai jirage zuwa sararin samaniya ko kuma sama jannati, wato nan da shekaru goma masu zuwa.

Jaridar Izvestiya da ake wallafa a kullum, ta ruwaito cewa, kasafin kudin da aka warewa tashar daga wannan shekare zuwa shekara ta 2025 ya kai dala biliyan 3.3 ko kuma kusan dala miliyan 330 a kowace shekara.

Hakan na nufin an samu ragin kashi goma cikin 100 daga daftarin da aka tsara tun a watan Aprilun bara.

Hukumar da ke kula da ayyukan zuwa sama jannati na Rasha na daga cikin wuraren ayyuka guda biyar da take da su, wadanda ta ke aiki tare da ma’aikata daban-daban domin gudanar da bincike.

Rasha na taka muhimmiyar rawa wajen safarar kwararrunta daga doron kasa zuwa sararin samaniya, tun bayan da Amurka ta janye kayayyakin aikinta da kwararrunta daga tashar.

Amurka dai ita tafi kowace kasa kashe kudaden raya wannan tasha tun bayan da ta kaddamar da ayyukanta a shekarar 1998, inda take kashe dala biliyan uku a duk shekara.

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG