Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Kai Harin Makami Mai Linzami Kan Asibitin Yara A Ukraine


Ma'aikatan kashe gobara suna aiki a asibitin yara da Rasha ta kai hari
Ma'aikatan kashe gobara suna aiki a asibitin yara da Rasha ta kai hari

Rasha ta kai hari da makami mai linzami kan wani asibitin yara da ke babban birnin Ukraine a jiya Litinin, daya daga cikin hare-haren da ta ke kaiwa a yankunan kasar da ya wuce gona da iri, harin dai ya yi sanadiyar mutuwar mutane 31 tare da jikkata wasu 154.

Jami'an Ukraine sun ce Rasha ta kai hari kan babban birnin kasar Kyiv da wasu garuruwa hudu da suka hada da - Dnipro, Kryvyi Rih, Slovyansk da kuma Kramatorsk.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya ce Rasha ta kai hare-hare da rana da makamai masu linzami sama da 40 a biranen biyar, harin da ya afka kan wasu gidaje da kayayyakin more rayuwa. Sojojin saman Ukraine sun ce sun kakkabo makamai masu linzami guda 30.

Ma'aikata suna share gadaje a wani dakin da ya rufta a harin da Rasha ta kai asibitin kananan yara
Ma'aikata suna share gadaje a wani dakin da ya rufta a harin da Rasha ta kai asibitin kananan yara

Kakakin Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya ce, Sakatare-Janar din Antonio Guterres ya yi Allah wadai da hare-haren, yana mai cewa hare-haren da aka kai a cibiyoyin kiwon lafiya "abin damuwa ne matuka"

Ita ma Amurka ta yi Allah-wadai da harin da Rasha ta kai a asibitin yara da ke birnin Kyiv da sauran wurare.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG