Su dai masu shigar da kara sun nemi da a yanke mai hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru biyar
Kamfanin Dillancin Labaran na Interfax ya ruwaito wani Lauyan Navalny ya na cewa hukuncin zai iya hana shi takarar zaben shugabancin kasar.
Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin bai bayyana ko zai sake tsayawa takarar kujerarsa ba.
Navalny ya fito idon duniya ne bayan da ya fallasa almundahanar da ake yi a wasu ma'aikatun gwamnatin kasar.
Shi ne kuma ya jagoranci zanga zanga a shekarun 2011 da kuma 2012 wacce ta hade kai wajen kalubalantar dawowar Putin kan karagar mulki.
Navalny ya ce zai ci gaba da harkokin siyasarsa duk da hukuncinsa da aka yanke masa.