Kasar Rasha tace tana bukatar ta yi nazarin hukuncin da kwamitin gasar wasannin Olympics na kasa-da-kasa da ake kira IOC a takaice ya dauka na hana kasar ta Rasha shiga gasar wasannin motsa jiki na Olympics na hunturu wanda za a yi a Pyeongchang dake Korea ta kudu kafin ta dauki wasu matakai.
Mai Magana da yawun fadar shugaban Rasha Dmitry Pescov ya fadawa manema labarai a yau laraba cewa muhimmin abu a yanzu shine kare hakkokin ‘yan wasan Rasha.
Kwamitin na IOC ya yanke hukunci jiya Talata cewa ‘yan Rasha zasu iya shiga gasar a matsayin ‘yan wasa daga Rasha amma ba a matsayin kasa ba.
Facebook Forum