Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan da takwaran aikinsa na Rasha Vladimir Putin sun ce sun cimma wata jituwa wadda ta kau da yiwuwar kai farmaki kan tungar 'yan tawaye da ke Idlib a kasar Siriya.
"Za mu kau da matsalar jinkai wadda kan faru muddun aka dau matakin soji," a cewar Shugaba Erdogan bayan tattaunawar ta jiya Litini a yankin shakatawar nan na Sochi da ke gabar ruwa a Rasha.
Shugabannin kasashen biyu sun amince su ware yankin da ba a harkokin soji a ciki mai girman kilomita 20 murabba'i a cikin kasar Siriya. Shugaba Putin ya ce wannan yarjajjeniyar za ta kau da barazanar da filin jirgin saman sojojin Rasha da ke Hmeimim, wanda 'yan tawayen su ka sha aunawa, ciki har da amfani da jirage marasa matuka.
Facebook Forum