Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Talata Za'a Soma Duban Watan Sallah A Najeriya


Za'a soma duban jinjirin watan Shawwal a ranar Talata a Najeriya, yayin da shugaba Muhammadu Buhari zai gudanar da sallar idi a fadar shugaban kasa, tare da bin ka'idojin yaki da cutar coronavirus.

Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harakokin addinin Musulunci a Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya yi kiran da a soma duban jinjirin watan Shawwal daga ranar Talata a duk fadin kasar.

Wata sanarwa da mataimakin sakataren majalisar kolin ta harkokin addinin Musulunci Farfesa Salisu Shehu ya fitar, ta ce ranar Talata 11 ga watan Mayun shekara ta 2021, ita ce rana ta 29 ga watan Ramadan, shekarar Hijrah 1442, haka kuma ita ce ranar farko ta dunan jinjirin watan sallah (Shawwal).

Ganin sabon watan na Shawwal ne zai kawo karshen azumin watan Ramadan da al'ummar musulmai suke kwashe tsawon wata daya suna yi a kowace shekara, da kuma gudanar da bikin sallar idil-fitr, kamar yadda yake kunshe a dokokin addinin Musulunci.

Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar III
Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar III

Idan kuma ba’a sami ganin watan a ranar Talata ba, hakan na nufin watan Ramadan zai yi ‘farilla’, wato za’a yi azumi 30, kana a yi sallar idi a ranar Alhamis, wadda za ta kasance 1 ga watan Shawwal.

To sai dai sanarwar ta bukaci al’ummar Musulmai da su soma duban watan a ranar Talata 29 ga Ramadan, haka kuma a gaggauta kai tabbatacce kuma sashihin rahoton ganin watan ga uban kasa ko hakimi mafi kusa, domin isarwa ga kwamitin duban wata na majalisar sarkin musulmi.

Karin bayani akan: Musulmai, Ramadan, Farfesa Salisu Shehu, COVID-19, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Sanarwar ta ci gaba da cewa mai alfarma sarkin musulmi ya yi kira ga daukacin jama’a da su ci gaba da yin addu’o’in samun zama lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.

A daya bangaren kuma shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari, ya bukaci ‘yan kasar da su yi kaffa-kaffa a bukukuwan sallar idi na bana, kasancewar har yanzu ana cikin annobar COVID-19.

Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

Akan haka ne ma shugaban kasar zai gudanar da sallar idi tare da iyalansu da manyan jami’an gwamnatinsa a cikin fadar shugaban kasa da ke Abuja, tare da bin dukkan sharuda da dokokin yaki da cutar ta korona.

Bayan wannan kuma, an soke kai gaisuwar sallah da bisa al’ada shugabannin addini da na al’umma da ma na siyasa suke kai wa shugaban kasa.

XS
SM
MD
LG