Abokin aikinmu Ibrahim Garba ya tattauna da wani matsakaicin masana’anci Alhaji Jibrin Tafida, don jin ci gaban da aka samu tsakanin ranar ta yau da bikin ranar da aka yi a baya a Amurka. Inda ya fara da cewa, masu masana’antu a nahiyar Afirka na fuskantar matsalolin bunkasar matsakaita da manyan masana’antu.
Sannan hakan na faruwa ne kasancewar duniya ta kara yawan jama’a da kuma kalubalen yanayi da makamantansu. Yayi kira ga gwamnatoci da su taimakawa matasa da mata game da samanr da ayyukan yi. Yace idan aka bawa mace aikin yi kamar k aba duk al’umma ne.
Idan kuma ka bawa matasa aikin yi, to ka taimakawa zaman lafiya, domin kuwa idan matasa ba s u da abin yi to komai na iya faruwa da yanayion tsaron kasa. Ana iya sauraron cikakkiyar hirar ta hanyar latsa maballin sautin da ke kasan labarin.