Farfesa Suleiman Khalil, shugaban tsangayar zamantakewa ta jami’ar Usman Danfodio dake Sokoto yace dukan addinai da al’ummomin duniya, da akidojin jama’a na kokari su karfafa batun hakuri a cikin jama’a, saboda wannan na da muhimmanci a zamantakewar bil’adama.
Ya kuma ce a koda yaushe yana da kyau mutum ya kasance mai hakuri da hali ko yanayin da ya sami kansa, saboda a sami zaman lafiya da kyakkyawan zamantakewa.
Najeriya kasa ce mai addinai, da kabilu, da al’adu da al’ummomi dabam dabam. Farfesa Khalil ya cigaba da cewa hakuri shike rike al’umma, musamman a kasa kamar Najeriya akwai bukatar a karfafa wannan batu. Yawancin lokuta akan sami rikici tsakanin al’umma amma daga karshe hakuri ne kadai zai warware komai.
Ga karin bayani cikin sauti daga Hassan Uamr Tambuwal.
Facebook Forum