Janar Minimah wanda yanzu ya zama tsohon hafsan sojojin Najeriya ya shaidawa kwamandojin dake halartar taron sojojin cewa mayakan Najeriya sun 'yanto duka sassan dake hannun 'yan Boko Haram a shiyar arewa maso gabas.
Ya sanar da cewa dakarun kasar na shirin yiwa dajin Sambisa kawanya domin kai da harin da zai sa a yi masa kwaf daya domin 'yanto dajin da mutanen dake ciki daga hannun 'yan ta'adan.
Janar Minimah yace sha'anin tsaro ba na jami'an tsaro ne kadai ba amma wani alamari ne da ya shafi kowa da kowa. Ya roki 'yan Najeriya da su lura da duk wani abun dake faruwa tsakaninsu a cikin motocin safa safa ko a kasuwanni. Ya umurci a gujewa wuraren da mutane ke taruwa ko wuri mai cunkoson jama'a. Yace kowa yayi takatsantsan da danuwansa a wannan hali da ake ciki.
Akan yadda har yanzu ana samun karuwar kunar bakin wake duk da ikirarin cewa ana samun galaba akan 'yan Boko Haram sai hafsan yace kasancewar an tarwatsasu da karfin soja yanzu basa iya yin fito na fito dalili ke nan da suke kai hare haren kunar bakin wake da yin yakin sari ka noke.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.