Mutane da dama a jihar ta Edo sun bayyana ra'ayin cewa an gudanar da zaben cikin lumana, inda wasu mazauna jihar suka yabawa hukumar zabe da jami’an tsaro a kan irin rawar da su taka wurin tabbatar da zaman lafiya kafin zabe da lokacin zaben da ma bayan zabe.
Wasu al’ummar jihar sun zargi tsohon shugaban jami’iyar APC ta kasa Adams Aliyu Oshiomole da yunkurin kassara jihar ta Edo, a cewar wani da ake kira Monday.
Magoya bayan gwamnan da dama ne suka bayyana matukar farin ciki akan nasarar da Gwamnan jihar Edo kuma dan takarar DPD a zaben kujeran gwamnan, Mr Godwin Obasake ya yi.
Shi dai Obaseki na neman wa’adi na biyu ne domin a shekarar 2016 ya lashe zabe karkashin jam’iyyar APC.
‘Yan jami’iyar DPD da ta lashe zaben sun ikirarin cewa basu rarraba kudi ba domin sayin kuri’u daga jama’a, wanda hakan ke nufin mutane sun yaba da aikin su.
Wani dan jami’iyar APC a jihar, Alhaji Muhammad Fanga a kasuwar timatiri, ya ce "duk dan siyasa da ya shiga takara ya san akwai nasara kana akwai akasin haka, amma abu mai muhimmanci shine an yi zabe lafiya."
To sai dai wasu 'yan jami’iyar ta APC sun yi korafin cewa akwai wasu wurare da ba a yi musu adalci ba amma duk da sun gargadi jama’a da su rungumi kaddara.
Wani jami’in sa ido a kan zabe daga kungiyar “Citizen Rights for Leadership and Peace” Komred Zuberu Ladan, ya ce wannan zabe tabbaci ne na’yanci . Ya ce mutane sun fito sun kada kuri’a a wannan zabe.
Ga dai rahoton Lamido Abubakar daga jihar ta Edoi:
Facebook Forum