Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra'ayin Wani Tsohon Dan Siyasa Kan Ranar Dimokradiyya a Najeriya


Alh. Hamza Usman Darma
Alh. Hamza Usman Darma

Yadda shugaba Muhammadu Buhari ya mayar da ranar 12 ga watan Yunin kowacce shekara a matsayin ranar dimokradiyar Najeriya maimakon ranar 29 ga watan Mayu da aka saba, wata hanya ce ta nuna cewar siyasa ta samu wajen zama a kasa baki daya.

Ko da yake wasu suna ganin wannan yunkuri don a nuna cewar 12 ga watan Yunin wata hanya ce ta amincewa da marigayi MKO Abiola ne ya lashe zaben shugabanci a shekara ta 1993.

Masu fashin bakin sun bayyana cewa a tsawo lokaci wasu sassan kasar nan ke fafutukar tabbatar da cewar an ware wannan rana a matsayin wata rana ta mussaman.

Akan haka ne wakiliyar Dandalin VOA ta zanta da wani dan siyasan na wancan lokaci, Alhaji Hamza Usman Darma don mu ji ko ya gamsu da yadda dimokradiya ke tafiya a Najeriya, inda ya ce kwashe shekaru 20 da aka yi bayan komawa turbar dimokradiya a Najeriya wani muhimmin ci gaba ne ga kasar.

A saurari cikakken rahoton wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:08:13 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG