Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pompeo Ya Zargi China Da Yi Wa 'Yan Jarida Katsalandan a Hong Kong


Sakataren Harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo
Sakataren Harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya ce ya lura cewa gwamnatin China ta yi barazanar yin katsalandan kan aikin 'yan jaridar Amurka a Hong Kong.

A cewarsa, duk wani kuduri da ya shafi ‘yancin gashin kan Hong Kong, zai iya shafar yadda Amurka take kallon yankin na Hong Kong.

A cikin wata sanarwa da aka fitar, Pompeo ya ce "wadannan 'yan jaridan, mambobi ne na' yan jaridu masu ‘yanci, ba masu yada farfaganda ba ne, kuma rahotanninsu suna da mahimmanci wajen ilmantar da al'umar kasar China, da ma duniya baki daya.

A dai shekarar 1997, Birtaniya ta mika wa China yankin Hong Kong, kuma an yi ma yankin alkawarin "cikakken ikon cin gashin kai" na tsawon shekara 50.

Abin da ya bai wa yankin wani mukami na musamman karkashin wata dokar Amurka, wacce ta ba yankin damar zama cibiyar kasuwanci a duniya

A ranar 6 ga watan Mayu, Pompeo ya sanar, da cewa, ma’aikatar harkokin wajen Amurka na jinkirta wani rahoto da za ta mika wa majalisar dokokin kasar, kan ko Hong Kong na cin moriyar cikakken ‘yancin gashin kai daga China – abin da zai ba yankin damar samun ci gaba da zama ‘yar lelen Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG