Friministan kasar Pakistan ya bayyana cewa kungiyoyin ayyukan leken asirin kasa da kasa, suma suna da nasu laifin wajen gaza baiwa Pakistan hadin kan kaiwa ga kame Osama bin Laden, a dai dai lokacin da kasa da kasa ke ci gaba da takurawa Pakistan kan sai tayi cikakken bayanin yadda jagoran kungiyar al-Qaida ya jima yana zaune a garin da mafi yawan mazauna cikinsa jami’an soja ne.
Friministan Pakistan Yousuf Reza Gilani, yau laraba a birnin Paris na Faransa aka ji yana cewa idan har Pakistan tayi kuskuren gaza kamo Osama bin Laden, ai suma jami’an ayyukan leken asirin kasa da kasa suna da nasu kuskuren na kin jan hankali Pakistan tun da wuri.
A daren lahadin da ta wuce ne sojin kundunbalar Amurka na musamman,suka afkawa gidan da bin Laden ke zaune suka kashe shi a garin Abbottabad.
Jami’an Amurka sun bukaci da sai lallai hukumomin Pakistan suyi cikakken bayani kan yadda har aka sake jagoran na kungiyar al-qaida zai zauna a gida mai tsadar da kudinsa ya kai Dola miliyan guda ba tare da sanin hukumomin Pakistan ba.
Shima jami’in dake Magana da yawun ma’aikatar tsaron kasar Afghanistan dake makwabtaka da Pakistan, yayi zargin cewa tilas ne ma’aikatan ayyukan leken asirin kasar Pakistan, su kasance suna da labarin Bin Laden na zaune a gidan da aka kashe shi domin gidan yana kusa ne da barikin soja.