Wannan ya biyo bayan damuwa da shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, ya yi na nuna hakan ba zai yiwu ba don babu bangare a PDP balle kuma a samu sauya sheka.
Effiong dai ya dage cewa jam’iyyar ta rabe gida biyu. PDP dai ta ci gaba da zargin jam’iyyar APC da neman mayar da Najeriya mai bin jam’iyya ‘daya, don haka ta hana PDP dinke baraka.
Sakataren kwamitin rikon jam’iyyar PDP, Abdul Ningi, na ganin wannan fada da ake yi a jam’iyyar shine ke kawo koma baya ga jam’iyyar. Haka kuma ya zargi cewa da akwai hannun baki cikin fadan, kuma y ace ba zasu yard aba ace jam’iyya ‘daya ce tal ke mulkin Najeriya.
Sai dai kuma jam’iyyar APC ta yi watsi da wannan zargi da nuna PDP ba wata barazana ba ce a zaben shekara ta 2019.
Sakataren jam’iyyar APC na ‘kasa Maimala Buni, ya ce babu bukatar raba kawunan ‘yan PDP, domin kuwa suna hade lokacin da suka sha kaye, kuma mutanen na ‘kaura da jam’iyyar ne saboda abin kunya da suka yi na tsawon shekarun da suka kwashe suna kan mulki, amma sai yanzu ‘yan Najeriya ke ganin canji.
Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Facebook Forum