An mikawa gwamnan jihar Alhaji Hassan Ibrahim Dankwambo takardar amincewa ya zama dan takarar jam'iyyar a zaben da za'a yi a shekarar 2015, shi da shugaban kasa Dr. Goodluck Ebele Jonathan.
'Yan jam'iyyar sun yi dandazo ne domin su taya gwamnan murna , shi da mataimakinsa. Da amincewar, duk wani dan jam'iyyar mai kwadayin kujerar gwamnan sai ya hakura.
Sanata Joshua Lidani shi ya gabatar da jawabin mika takardar kudurin ta zarce wa gwamnan. Yace gwamna Dankwabo shi ne dan takara daya tilo na jam'iyyar a jihar Gombe. Yace kamar yadda suka amincewa shugaban kasa haka ma suka zo Gombe domin su tabbatarwa gwamnan cewa sun amince ya zarce.
A nasa jawabin gwamna Damkwambo ya yaba da bukatar. Yayi godiya ga jam'iyyar tare da gudummawa da take bashi amma yace zai tuntubi jama'ar jihar da amincewarsu. Ya yiwa shugaban kasa godiya tare da fatan alheri.
Wani mai sharhi akan alamuran yau da kullum Danjuma Muhammed yace tsayar da dan takara ba tare da amincewar jama'a ba ya sabama tsarin mulki da tsarin dimokradiya. Ya sabama kundun tsarin mulkin kasar Najeriya. Duk wadanda suka taru suka yi hakan sun yi cin amana. Bisa ga kundun tsarin mulki jama'a ke da ikon zaban wanda zai tsaya zabe domin ya mulkesu.
Idan har an san mutum yayi aiki to menene kuma ake tsoro. A fito fili a fafata tare idan yaci sa ya zarce din. Duk wanda yake da kwadayin son tsayawa kada a tauye masa hakinsa. Abun da suka yi wani sabon coge ne.
Amma Ahmed Abubakar Kwandos yace akwai basira a cikin shirin da jam'iyyar tayi. Yace idan aka duba shekaru uku da suka gabata mutanen Gombe sun sha kiran shi gwamnan ya bar aikinsa na akanta janaral ya nemi kujerar gwamna. Yace sun kai watanni tara suna nemansa suna kiransa. Duk abun da kowa ke bukata gwamnan ya yi masu.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammed.