Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP Ce Ta Raba Kanta Ba APC Ce Ta Rabata Ba - Mai Mala Buni


Sakataren APC na kasa Mai Mala Buni
Sakataren APC na kasa Mai Mala Buni

Sakataren jam'iyyar APC na kasa Mai Mala Buni ya musanta zargin cewar jam'iyyarsu ce take haddasa rikicin dake wakana a jihar Ondo, jihar da zata yi zaben gwamnanta mako mai zuwa

A firarsa da Muryar Amurka sakataren jam'iyyar APC na kasa Mai Mala Buni yayi tsokaci akan korafe korafen da mutane keyi dangane da zaben da za'a gudanar a jihar Ondo.

Injishi duk wanda ya san yadda shugaban Najeriya Muhammad Buhari ke gudanar da mulki, ya san baya sa baki a harkokin zabe. Ya na son kuri'ar kowa tayi tasiri a zabe. Baya bukatar a sa baki a harkar kowace jam'iyya.

Mai Mala Buni yace abun dake faruwa a Ondo yana faruwa ne tsakanin jam'iyyar PDP wadda ta raba kanta da kanta, ta haifar da bangarori biyu, na Makarfi da Modu Sheriff. Babu ruwan jam'iyyarsu, injishi.

Akan damar da kotun koli ta baiwa wani dan takarar PDP yaci gaba da daukaka kara a kotun daukaka kara yace su basu damu da wannan ba saboda duka abun dake kawo cikas kin bin kaida ne. Yace yayi imani hukumar zabe ka'ida take bi kuma babu abun da zai hanata aikata gaskiya.

Mai Mala Buni yace su ashirye suke su yi zabe kuma basu ga abun da zai kawi tsaiko ba.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:53 0:00

XS
SM
MD
LG