Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pascal : Tsohon Dan Wasan Super Eagle's Ya Lashe Zabe


Pascal Patrick
Pascal Patrick

An zabi tsohon dan wasan Super Eagle's Pascal Patrick a matsayin shugaban hukumar kula da wasan kwallon kafar Jihar Bauchi.

Pascal ya samu nasarar lashe zaben ne bayan da ya doke abokan takararsa biyu, wanda suka hada da tsohon shugaban hukumar ta FA a Bauchi, Yahuza Adamu Ningi, wanda ya shafe shekaru da dama yana jagorancin hukumar da kuma Zailani.

Zaben wanda akayi a ranar Litinin 10 ga watan Yuni 2019, ya gudana a dakin taro na filin wasa na tunawa da Sir. Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi a tarayyar Najeriya, wakilai 26 suka jefa kuri'u.

Pascal Patrick ya samu kuri'u 13, Zailani ya samu kuri'u 8, Yahuza kuri'u 3. Tsohon dan wasan na Najeriya yana daya daga cikin masu tsare tsare a kungiyar kwallon kafa ta Super Eagle's, a yanzu haka kafin kasance warsa a wannan matsayi.

Pascal ya fafata wasa tun daga matakin jiha inda ya fara daga kungiyar kwallon kafa ta Bauchi Wunti, da kuma Wikki Tourist, Gombe United sai Shorting Star FC Ibadan 1993/1996.

Ya kuma taka leda wa kungiyar kwallon kafa ta tawagar Najeriya.

Daga bisanin ya ketara kasashen waje inda ya samu nasara da dama tun daga kulob din KSV Waregem, Gençlerbirliği Ankara, da wasu kungiyoyi har zuwa 2006–2009 FC Apollo.

Nielse kafin ya ajeyi takalman wasansa yaci gaba da bada gudumawarsa ga fannin kwallon kafa daga mataki jiha da tarayya, inda ya taba rike shugaban kungiyar Wikki Tourist, Fc Bauchi.

Bayan zaben da aka masa na shugaban FA na Jihar Bauchi, Pascal yayi alkawalin dawo da Martabar wasan kwallon kafa a jihar Bauchi sakamakon koma baya da ta samu a shekarun da suka gabata.

Haka kuma yace babban abunda yake gaban su shi da wanda aka zaba shine, samun matsugunni na dindindin wa hukumar a matakin jiha wanda ta rasa a baya.

Daga karshe ya bukaci al'ummar jihar da su bashi goyon baya wajan ciyarda fannin wasan kwallon kafa gaba a jiha, ya kuma yi godiya wa wadan da suka zabeshi da waddan da suka taimaka masa wajan zaben nasa

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG