Kasar Pakistan ta sassauta ma wasu bangarori na kamfanoni dokar hana zirga-zirga, saboda su samu su koma harkokinsu.
Amma ta tsawaita wa makarantu da kuma masu tarurruka dokar da makonni biyu, saboda a takaita yaduwar cutar coronavirus.
Firaminista Imran Khan ya bayyana wannan shawarar da aka yanke, bayan da ya jagoranci wani taron manyan jami’an gwamnatinsa.
Yayin taron an kuma yi nazarin dokar killacewa a kasar mai mutum miliyan 220, wacce ya kamata a ce wa’adinta ya kare da karfe 12 daren jiya Talata.
Adadin wadanda suka kamu da cutar a kasar ya kai 6,000, a yayin da kuma wadanda suka mutu ya kai wajen 100.
Duk da rashin yaduwar cutar sosai a kasar idan aka kwatanta da wasu kasashen, kwararru da kuma jami’an gwamnati sun yi gargadin cewa adadin na iya matukar karuwa cikin kwanakin da ke tafe.
Facebook Forum