Majalisar Dattawan Najeriya ta garzaya zuwa kotun kolin kasar domin kalubalantar matakin da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka na dakatar da babban Alkalin kasar Walter Onnoghen.
Wata sanarwa dauke da sa hannun mai bai wa shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki shawara kan harkokin yada labarai, Yusuph Olaniyonu, wacce aka wallafa a shafin Twitter na ofishin shugaban majalisar, ta nuna cewa ana kalubalantar Buhari ne kan batutuwa biyu.
“Majalisar ta shigar da kara a kotun kolin ne domin ta nemi karin bayani kan ko matakin da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka na dakatar da babban Alkalin Najeriya, Walter Nkannu Onnoghen, ya saba dokar kasa,” kamar yadda sanarwar ta nuna.
Sannan majalisar har ila yau ta nemi kotun ta fayyace mata “ko matakin na shugaban na Najeriya ya shiga hurumin majalisar kamar sashi na 292 a kundin tsarin mulkin kasar,” ya nuna ita ce take da hurumin daukan wannan mataki.
Dalilin wannan kara da majalisar ta shigar, ya sa ta dauki matakin soke zaman da ta shirya yi a ranar Talata domin yin muhawara kan dakatar da Onnoghen a cewar sanarawar.
"An dage zaman majalisar da aka tsara za a yi a gobe (Talata)."
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wani martani da fadar gwamnatin ta Najeriya ta mayar dangane da karar da aka shigar da ita.
A makon da ya gabata aka dakatar da babban Alkali na Najeriya bisa zargin kin bayyana daukacin kadarorin da ya mallaka, lamarin da ya sa aka shigar da shi kara a gaba kotun da’ar ma’aikata.