Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ofishin Jakadancin Najeriya Ya Mayarda Martani Kan Kalamun Sanato Cruz


Shugaban Najeriya da shugaban Amurka
Shugaban Najeriya da shugaban Amurka

Ofishin Jakadancin Najeriya ya mayarda martani dangane da batancin da Sanato Cruz ya yiwa Najeriya cikin kalamunsa a jihar Texas.

Ofishin jakadancin najeriya a nan Amurka ya bayyana fushinsa a kan kalaman dan majalisar dattijai mai wakiltar jihar Texas Ted Cruz cewa, ana samun matsala da sabon dandalin rajistar inshoran kasar ne sabili da an dauki ‘yan sanen yanar gizo na najeriya aiki a wurin.

A cikin hirarshi da sashen Hausa mataimakin jakaden najeriya a nan Amurka B.E. Archibong ya bayyana cewa, ko da yake wadansu kafofin sadarwa sun ce ba a dan majalisar yake yi, yace idan ma wasa ne do kuwa wasan ya wuce gona da iri.
“kamar kowanne dan najeriya da ya san ya kamata, hankalinmu ya tashi kwarai da wadannan kamalaman na Ted Cruz, ko da yake wadansu jaridu sun ce wasa yake yi, amma a ganina, wasan ya wuce gona iri. Musamman yin amfani da ‘yan kasar dake da kaunar zaman lafiya wajen bayyana abinda ya shafi siyasar cikin gida ta Amurka.”
Grace ta tambaye matakin da ofishin jakadancin ya dauka domin nuna rashin gamsuwarshi a kan wannan musamman ga ofishin dan majalisar sai jakade Archibong ya bayyana cewa,” I, zamu aika mashi da korafinmu, kuma tuni muka fitar da sanarwar inda muka bayyana rashin gamsuwarmu da kalamanshi wanda bai kamata a ce ya fito daga dan majalisar dattijan Amurka ba musamman a wannan lokacin da aka daga matsayin dangantakar kasashen biyu zuwa mataki mafi girma. Kimanin wata guda ke nan da ya shige da shugaba Goodluck Jonathan ya zo birnin NY ya kuma gana da shugaba Barack Obama inda suka tattauna ka batutuwa dabam dabam da suka kara taimakawa wajen kara dankon dangantaka tsakanin kasashen.”

Na kuma tambaye shi cewa, akwai ‘yan Najeriya da suke cewa lallai ne dan majalis Ted Cruz ya fito ya roki ‘yan Najeriya gafara, ko ofishin jakadancin yana da wannan ra’ayin sai ya bayyana cewa.

S.O.T
Ina jin suna da gaskiya, suna da gaskiya, al’ummarmu suna da gaskiya idan suka yi haka. kowa yana da ‘yanci daukar matakin da doka ta kayyade ya bayyana rashin gamsuwarshi, suna iya bayyana haka ta dandalin sadarwa da makamantan haka suna da ‘yancin yin haka babu wanda zai hana su.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG