Obasanjo, ya ce ya kamata mu fadawa kasashen duniya cewa matsalar Najeriya ba wai ‘yan kasar ba zasu iya rike kansu bane, matsalace ta tsaro da ta kawo cikas wajen gudanar da harkokin rayuwa musamman ma ta harkokin Noma.
Cibiyar bincike kan ayyukan gona ta IITA, itace ta samar da wannan sabon iri da Obasanjo ya mikawa manoman ta hannun gwamnatin jihar Borno, wanda suka hada da irin Gero da Dawa da Masara da Alkama da Shinkafa da Wake da kuma Waken Suya.
Obasanjo, yace karancin abinci da ake fama da ita a jihar Borno, ba wai don ragwantaka da mutanen Borno ke ita bane, saboda suna da matsala ne wadda kuma dole sai an tabbatar da cewa an magance matsalar baki ‘daya.
Da yake jawabi gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, yace akwai wasu abubuwa uku da Obasanjo ya ke mayar da hankali akai, na farko shine yana tsaye wajen tabbatar da hadin kan Najeriya, haka kuma mutum ne mai daukar matsaya a duk lokacin da aka shiga wata matsala, haka zalika ba a barshi a baya ba wajen harkokin Noma a wannan ‘kasa.
Gwamna Shettima, ya ce babu wata jiha a Najeriya da zata ce ta shirya harkokin noma fiye da jihar Borno. Ya ce sun saka kudi masu yawa a harkokin noma da kiwo, kuma yanzu haka ana kokarin samarwa da mutanen jihar taki don ci gaba da harkokin nomansu.
Domin karin bayani ga rahotan Haruna Dauda Biu.
Facebook Forum