Shugaban Amurka Barack Obama, ya tsoma baki cikin zazzafar muhawara da ake yi a Britaniya kan kuri'ar raba gardamar da 'yan kasar zasu ranar 23 ga watan Yuni, kan ko kasar zata ci gaba da zama cikin kungiyar tarayyar turai.
"Bana jin kungiyar tarayyar Turai tana rage tasirin Britaniya a duniya, sai dai ma ace tana kara bunkasa shi," inji shugaban na Amurka, a wani taro da manema labarai na hadin guiwa, da PM Ingilan, David Cameroon, bayan da suka gana jiya jumma'a.
Kalaman na Mr. Obama, ya karawa shugaban na Britaniya kwarin guiwa, kan matsayarsa na goyon bayan kasar ta ci gaba da zama cikin kungiyar tarayyar turai.
Amma kalaman na shugaba Obama sun harzuka masu adawa da wannan shiri a Ingila, wadanda suke ganin maganar da shugaban na Amurka yayi, shishshigi ne, cikin harkokin cikin gida na kasar.
A cikin wata makala da aka wallafa a jaridar "The Telegraph," da saukar jirgin saman shugaban na Amurka a daren Alhamis, a wata tashar jirgin sama dake bayan garin London, shugaban na Amurka, yayi kira ga Britaniya ta ci gaba da zama wakiliya a kungiyar tarayyar turai.
Dangantaka tsakanin Amurka da Britaniya, shine mu'amala da shugabannin a Washington suke da ita, da kasar Ingilan tun zamanin mulkin Winston Churchil, wacce ake dauka a zaman "ta musamman ce," kuma Amurka tana kallon ci gaba da kasancewar kasar cikin kungiyar, tamkar wakilci ne ga Amurka a kungiyar hada kan kasashen turan, mai wakilai 28.