Inda ya kara godewa ‘yan wasan kasar har ma da ‘yan wasan nakasassu bisa kwazonsu. Ya bayyana cewa yan wasan suna wakiltar katafariyar kasar Amurka mai albarka.
Kasar da ke bada daga ga ‘ya’yanta ba tare nuna wariyar akan asalin inda suka fito ba. Matukar mutum na da tarbiyya da hangen mnesa da kuma kishin kasar.
Wannan wasan Olimpiya shine na farko da wata kasar Kudancin Amurka ta karbiu bakuncinsa. Ya kara dac cewa, ‘yan wasanni daban daban na Amurkar sun fito ne daga jihohi 46.
Sai kuma babban birnin tarayya wato nan Washington da kuma yankin tsibirin da ake cewa Virgin Islands. Karshe shugaban ya rufe da cewa, su je su kwaso gwala-gwalen lambobin yabo.