WASHINGTON D.C. —
Kamar yadda watakila wasu daga cikin masu sauraron mu suka ji a makon da ya gabata, muna tattaunawa da Alhaji Sule Aliyu Kanya, manomi da ya shafe sama da shekara 20 yana noma a Najeriya, wanda ya fara yi mana karin bayani kan irin kalubalen da manoma suke fuskanta daga wasu makiyaya, da yadda suke samun amfanin gona a da, da suke amfani da taki na gargajiya.
A cikin shirin mu na wannan makon, wakiliyarmu a Abuja Hauwa Umar, ta fara da tambayarsa kamar haka…...